in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bude taron ministocin harkokin wajen kungiyar 'yan ba ruwanmu karo na 16
2012-08-29 10:35:02 cri

Jiya ranar 28 ga wannan wata, aka bude taron ministocin harkokin waje na taron kolin kungiyar 'yan ba ruwanmu karo na 16 a Tehran, babban birnin kasar Iran (wato Farisa) domin share fage ga taron shugabannin kungiyar da za a yi nan ba da dadewa ba.

Muhimmin aikin wannan taron ministocin harkokin waje shi ne yin tattaunawa kan shirin kudurin da aka zartas a yayin taron manyan jami'ai na taron kolin kungiyar tare kuma da gabatar da sakamakon tattaunawa ga taron shugabannin da za a yi. A yayin bikin bude taron, mataimakin ministan harkokin wajen kasar Masar Ramzy Ezz El Din ya ce, za a yi taron shugabannin kungiyar 'yan ba ruwanmu na wannan karo a lokacin da yanayin kasa da kasa ke yin manyan sauye-sauye, yana fatan kungiyar za ta taimaka yadda ya kamata yayin da ake fuskantar kalubale.

Za a shafe kwanaki biyu ana yin wannan taron ministocin harkokin waje, kafin wannan, an kira taron manyan jami'ai, sannan kuma za a kira taron shugabannin kungiyar 'yan ba ruwanmu daga ranar 30 zuwa ta 31 ga wannan wata.

A Jiya Talata 28 ga wata ne, kakakin babban magatakardar majalisar dinkin duniya ya bayyana cewa, a wannan rana, Mr. Ban Ki-moon ya tashi zuwa Iran domin halartar taron shugabannin, kuma zai gana da shugabannin kasar a yayin taron.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China