130625_GulfGuineaAmi
|
An bude taron koli na tsawon kwanaki biyu don tattaunawa kan batun tsaro a tekun Gulf na Guinea, a ran 24 ga wata na agogon wurin a birnin Yaounde hedkwatar kasar Kamaru. Shugabannin kasashen tsakiya da yammacin Afrika da dama sun halarci taron domin tattaunawa kan wasu manyan batutuwa ciki hadda tabbatar da tsaro a tekun Gulf na Guinea, yaki da 'yan fashin teku da dai sauransu.
An ba da labari cewa, wannan shi ne karo na farko da aka kira irin wannan taro kan batun tsaro a tekun na yankin Gulf na Guinea, wanda ya samu halartar shugabannin kasashen ECOWAS da ECCAS da dama, ciki hadda shugabannin kasashen Nijeriya, Nijar, Sao Tome and Principe, Guinea Bissau, Benin, Burkina Faso, Chadi, Kwaddibuwa da sauransu. Ban da haka, MDD, AU, da ma kungiyar kula da harkokin sararin teku ta kasa da kasa, kwamitin kula da harkokin Gulf na Guinea da sauransu sun halarci taron.
A yayin taron, shugabanni da dama sun ba da jawabi kan jigon taron. Shugaban kasar Kwaddibuwa wanda ke rike da shugabancin karba-karba na kungiyar ECOWAS Alassane Ouattara ya yi nuni da cewa, ya kamata kasashen duniya su mai da hankali kan tsaron teku a Gulf na Guinea kamar yadda ake yi a Gulf din Aden dake gabashin Afrika.
Shugaban Kamaru Paul Biya a nasa bangare ya nuna cewa, dole ne kasashen duniya su dora muhimmanci kan barazanar da matsalar tsaro a tekun Gulf na Guinea za ta haifar, kana a kara karfin ba da tabbaci ga tsaron jiragen ruwa da za su ratsa wannan yanki ta yadda za a tabbatar da moriyar tattalin arzikin kasa da kasa.
A sa'i daya kuma, shugabannin kasashen yammacin Afrika sun yi kira da a kafa wata runduna a kan teku domin yaki da 'yan fashin teku a Gulf na Guinea.
A shekarun baya, an sha fuskantar matsalar tsaro wadda ta kara tsananta a wannan yanki, musamman ma matsalar 'yan fashin teku.
A cikin wani rahoton da kungiya mai kula da harkokin sararin teku ta kasa da kasa da dai sauran kungiyoyi suka bayar a makon da ya gabata, ta ce kalubalolin da ake fuskanta a Gulf na Guinea ya fi na Gulf din Aden tsanani, inda har ma wurin ya zama wani sabon sansanin 'yan fashin teku.
Wannan rahoto ya bayyana cewa a shekarar 2012, yawan ma'aikatan jiragen ruwa da suka gamu da hare-haren da 'yan fashin teku suka kai musu a yankin yammacin Afrika ya kai 966, yayin da a Gulf din Aden wannan adadi ya kai 851. Wannan shine karo na farko da wannan adadi a Gulf na Guinea ya fi na Gulf din Aden yawa.
Bugu da kari, wurin da ya fi fama da hare-haren da 'yan fashin teku suke kaiwa a wannan yanki shi ne gabar tekun kasar Nijeriya, saboda ganin cewa akwai jiragen ruwa da dama dake dauke da man fetur da suke fitowa daga wannan kasa. Akwai bambanci tsakanin 'yan fashin teku na Gulf din Aden da na Gulf na Guinea. 'Yan fashin teku a Gulf na Guinea a maimakon yin garkuwa da mutane domin neman kudin fansa, su kan yi kwasar ganima kan jiragen ruwan dauke da man fetur bisa matakin karfin tuwo mai tsanani, saboda ya fi sauri wajen samun kudi ta hanyar yin kwasar ganima, da kuma sayar da man fetur da suka kwace.
A ranar 13 ga watan Fabrairu na shekarar 2012, 'yan fashin teku guda 8 sun yi fashi kan wani jirgin ruwa mai suna "TianWei" na kasar Panama dake dauke da ma'aikatan Sinawa a tashar Lagos ta kasar Nijeriya, inda shugaban jirgin basine, Fan Shuren da wani dan lardin Taiwan suka mutu.
Kafofin yada labaru na ganin cewa, ko da yake, 'yan fashin teku a Gulf na Guinea suna cin karensu ba babbaka, to amma saboda matsalar 'yan fashin tekun Somaliya ta dade da jawo hankalin kasa da kasa, hakan ya sa, matsalar tsaro a tekun Gulf na Guinea ba ta jawo hankalin kasa da kasa sosai ba. An kira wannan taro ne a daidai wannan lokaci, wanda ya samu halartar shugabannin kasashen tsakiya da yammacin Afrika da sauran wakilan kungiyoyi a wannan yanki wanda ake ganin akwai ma'ana sosai kan hakan, abin da ya nuna cewa, kasashe da shugabannin da wannan batu ya shafa sun fahimci wajibcin yin hadin kai a fannin yin amfani da karfin soja tare, domin tinkarar 'yan fashin teku a Gulf na Guinea. (Amina)