in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Addinin musulunci ya sami yalwatuwa a kasar Sin
2011-09-14 15:12:18 cri

A cikin shekaru biyar da suka gabata, kungiyar addinin musulunci ta kasar Sin ta nuna kwazo da himma kan aikin bayanan addinin, kuma ta yi kokarin gyara kurakuren dake cikin littattafan addinin kuma ta yi bayani sosai kan abubuwan da suka shafi addinin, da haka, ta kiyaye babbar moriyar jama'ar kasa da kasar Sin, a sa'i daya kuma, ta kiyaye babbar moriyar musulman kasar Sin yadda ya kamata. Yin bayani kan addinin musulunci hanyar gargajiya ce da masu aikin sana'ar addinin musulunci na Sin suke dauka wajen yin farfaganda kan addinin, ma'anarsa ita ce kara karfa wa zuciyar jama'a domin su taimakawa juna da hana su yi laifi. Abubuwan da suka shafi aikin sun kumshi fannoni da yawa, misali, babban batun addinin musulinci da doka da biyayya da da'a da al'adu da tarihi da sauransu. Domin kara kyautata aikin, kungiyar addinin musulunci ta kasar Sin ta mai da hankali kan aikin horar da masu aikin kuma ta tsara tsarin aikin. Game da wannan, mataimakin shugaban kungiyar addinin musuluncin kasar Sin kuma babban sakatare Hong Changyou ya nuna cewa,  "A cikin shekaru biyar da suka wuce, muna kokarin kara zaman jituwar addinin da hada kan kabilu da zaman karko na zamantakewar al'umma, ban da wannan kuma, muna kokarin kara karfafa tunanin kishin kasa da hada kai da 'yan kasa da doka, a sa'i daya kuma, mun yi kokarin daidaita rikicin addinin musulunci da ya faru ba zato ba tsammani. Gaba daya, mun daidaita wasikun jama'a wajen 300 da suka shafi manufar addinin da harkokin addinin da ayyukan kananan kungiyoyin addinin musulunci na wurare daban daban da masalaci da abincin addinin musulmai da sauransu, hakan kuma mun warware sabane-sabanen zamantakewar al'umma iri daban daban cikin nasara."

Aikin haji shi ne babban aikin addinin musulunci da ake yi tsakanin kasa da kasa, a cikin wadannan shekaru biyar, kungiyar addinin musulunci ta yi kokarin kyautata aikin haji daga duk fannoni, yanzu dai, musulmai suna iya tafiya Makka daga kasar Sin kai tsaye, hakan kuma suna iya isa kasar cikin lokaci. Ban da wannan kuma, kungiyar ta yi kokarin kyautata sharadin sauka na masu yin haji, wato da, kowanen mutum yana sauka a wuri mai fadin muraba'in mita 3, yanzu dai, suna iya sauka a wuri mai fadin muraba'in mita 4. A shekarar 2007, an kara birnin Yinchuan da ya zama wurin tashin jirgin sama zuwa Makka kai tsaye. Kazalika, an yi kokarin kyautata sharadin likitanci. Hong Changyou ya nuna cewa,  "Kungiyar addinin musulunci ta Sin tana aiwatar da aikin haji bisa shirin da aka tanada. A cikin 'yan shekarun da suka gabata, yawancin musulumai sun saba da yin aikin haji tare, wani lokaci, musulmai fiye da goma kawai, amma mun mai hankali kan zaman lafiyar kowanen musunmi."

Kan batun cudanya tsakanin addinin musuluncin Sin da na kasashen waje, kungiyar addinin musuluncin Sin ta yi kokarin habaka sabbin hanyoyi bisa tushen sada zumunta na gargajiya, kuma ta nuna kwazo da himma domin yin cundaya da magana tsakaninta da na kasa da kasa. Hong Changyou ya bayyana mana cewa,  "Domin kara biyan bukatun sabon zamani, mun canja dabarun gargajiya, wato kai wa juna ziyara bisa gayyata. A shekarar 2009, kungiyar ta shirya "bikin nune-nunen al'adun addinai na kasashen Sin da Singapore" a kasar Singapore tare da sauran kungiyoyin addinai na Sin da Singapore. A shekarar 2010, ta shirya "bikin nune-nunen al'adun addinin musulunci na kasashen Sin da Indonesia" a Indonesia. A yayin bubukuwan da aka shirya, an nuna al'adun addinin musulunci da halin da musulman kasar Sin ke ciki sosai ga kasa da kasa."(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China