Da yake gabatar da su a gaban jami'an gwamnatin jihar Yobe a garin Damaturu, kakakin rundunar tsaron JTF a jihar, Laftana Eli Lazarus ya ce wadannan mutanen da aka sako ya nuna cewa, nan gaba kadan sauran da suka rage ma za'a sako su a mataki-mataki.
Da yake karbar wadannan mutane a madadin gwamnatin jihar ta Yobe, shugaban kwamitin lura da sake inganta rayuwar mutanen da ake tsare da su da gwamnatin jihar Yobe ta kafa, kuma babban jojin jihar mai shari'a Ahmad Mustapha Goneri ya godewa rundunar tsaron JTF bisa ga sako wadannan mutanen da suka yi, haka kuma ya ba su tabbacin cewa wadanda suka sako din za su gyara halayensu, ta yadda za su bayar da gudummawar su ga ci gaban kasa.
Shugaban kwamitin inganta rayuwar wadanda aka sako din ya kuma kara da cewa, gwamnatin jihar ta shirya tsaf don ganin ta tallafawa wadanda aka sako din ta dukkan hanyoyin da suka dace, don ganin sun gyara halayensu ta yadda za su fara sabuwar rayuwa wacce al'umma za su amince da ita.(Murtala)