in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sin ya gana da takwaransa na Nijeriya
2013-07-10 20:50:39 cri

A ranar Laraba 10 ga wata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi shawarwari da takwaransa na Nijeriya Goodluck Jonathan a babban dakin taron jama'a dake nan birnin Beijing, inda suka yi musayar ra'ayoyi kan bunkasa dangantaka tsakanin Sin da Nijeriya da kuma bunkasa dangantaka tsakanin Sin da kasashen Afirka baki daya, tare da samun daidaito tsakaninsu.

Shugaba Xi a bayanin sa,ya ce a cikin 'yan shekarun da suka wuce, dangantaka tsakanin Sin da Nijeriya tana bunkasa lami lafiya. Kasashen biyu sun hada gwiwa tsakaninsu a fannoni daban daban tare da samun babbar nasara. A cikin sabon yanayin da ake ciki kuma, Sin na fatan kara karfafa dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare tsakaninta da Nijeriya, da sada zumunci, da zurfafa hadin gwiwa irinta moriyar juna, da kara nuna goyon baya ga juna, a kokarin samun ci gaba tare da kawo alheri ga jama'ar kasashen biyu.

Shugaba Xi ya ba da shawarwari hudu kan yadda za'a karfafa dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare tsakanin Sin da Nijeriya.

Ta farko, karfafa mu'amala tsakanin manyan jami'an kasashen biyu, da ci gaba da fahimtar juna da ba da goyon baya ga juna kan batutuwan da suka shafi babbar moriyar kasashen biyu, da zurfafa amincewa da juna a siyasance da hadin gwiwa tsakaninsu.

Ta biyu, sa kaimi ga hakikanin hadin gwiwa tsakaninsu, a kokarin samun fasahohi daga juna da samun ci gaba tare. Kamata ya yi a kara hadin gwiwa a fannonin kafa manyan kayayyaki masu amfanin jama'a, cinikayya, zuba jari, makamashi da sauransu. Sin za ta ci gaba da kokari domin samun daidaito tsakanin bangarorin biyu a fannin cinikayya, da horar da gwanaye na Nijeriya. Ban da haka, gwamnatin Sin tana nuna goyon baya ga kamfanonin Sin da su zuba jari a Nijeriya, da sa kaimi ga kamfanonin da su koyar da mazauna wurin fasahohin zamani. Da fatan gwamnatin Nijeriya za ta ba da zarafi ga wannan batu.

Sai na uku inda yace a karfafa mu'amala a fannin al'adun dan adam, da kara sada zumunci tsakanin jama'ar kasashen biyu.

Sannan na hudu ya bukaci a karfafa hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu akan harkokin duniya da na shiyya shiyya, a kokarin kiyaye moriyar juna.

A nasa bangare kuma, shugaba Goodluck Jonathan ya bayyana cewa, dangantaka tsakanin Nijeriya da Sin tana bunkasa lami lafiya. Kasashen biyu suna hadin gwiwa tsakaninsu yadda ya kamata. Kasar Sin aminiya ce ta kasar Nijeriya, har ma ta dukkan kasashen Afirka baki daya. Nijeriya da kasar Sin suna da moriya iri daya. Shi ya sa za su hada gwiwa tsakaninsu yadda ya kamata. Kasar Nijeriya tana tsayawa tsayin daka kan sada zumunci tsakaninta da kasar Sin. Da fatan za a kyautata tsarin hadin gwiwa tsakaninta da Sin, da karfafa hadin gwiwar moriyar juna. Kasar Sin ta dade ta ba da goyon baya ga nahiyar Afirka. Wannan ya sa kaimi sosai ga tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali da samun ci gaba a nahiyar Afirka. A sabili da haka, kasar Nijeriya tana fatan kara azama kan zurfafa hadin gwiwa tsakaninta da Sin a kokarin samun sabon ci gaba.

Bayan shawarwarin, shugabannin kasashen biyu sun halarci bikin sa hannu kan bayanan hadin gwiwa a fannonin cinikayya, hada-hadar kudi, al'adu da sauransu tsakanin kasashen biyu.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China