in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Asusun IMF ya rage hasashen da ya yi game da ci gaban tattalin arzikin duniya
2013-07-10 10:19:52 cri

A ranar Talata ne asusun bayar da lamuni na kasa da kasa (IMF) ya rage hasashen ci gaban tattalin arzikin duniya da ya yi zuwa kashi 3.1 cikin 100 a shekara ta 2013, wato kasa da kashi 0.2 cikin 100 bisa hasashen da ya yi na watan Afrilu, saboda tafiyar hawainiyar ci gaban da aka samu a galibin muhimman kasuwannin kasashen da tattalin arzikinsu ke habaka a halin yanzu.

Wani rahoton da asusun ya fitar game da nazari kan tattalin arzikin duniya (WEO), ya bayyana cewa, koma bayan ci gaban tattalin arzikin duniya ya faru ne sakamakon karancin bukatun cikin gida da tafiyar hawainiyar ci gaban da aka samu a galibin muhimman kasuwannin kasashen da tattalin arzikinsu ke habaka a halin yanzu da kuma matsalar tattalin arzikin da ake fuskanta a kasashen EU.

Bugu da kari, asusun da ke da matsuguni a washington, ya sake yin kasa da hasashen da ya yi kan ci gaban tattalin arzikin duniya a shekara ta 2014 zuwa kashi 3.8 cikin 100 wato kasa da kashi 0.2 cikin 100 kan hasashen da ya yi na watan Afrilu.

Rahoton na IMF ya ce, galibin kasuwannin kasashen da tattalin arzikinsu ke habada a halin yanzu, suna fuskantar matsalolin tattalin arziki a kokarin bunkasa ayyukan tattalin arziki masu rauni da wadanda ke bukatar jari.

Asusun na IMF ya bayar da shawarar cewa, kamata ya yi kasashen da suka ci gaba, su rika taimakawa manufofin tattalin arzikin da shirye-shirye masu inganci da aka tsara da nufin bayar da rance na matsakaicin lokaci da gyare-gyaren da aka aiwatar don daidaita hanyoyin kashe kudade da bayar da rance. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China