in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Asusun bayar da lamuni na IMF zai taimakawa kasar Masar da rancen Dola biliyan 3 don farfado da tattalin arzikinta
2011-06-06 18:00:11 cri
Asusun bayar da lamuni na IMF ya ba da sanarwa a ranar Lahadi cewa, asusun da kasar Masar sun cimma yarjejeniyar da za ta kai ga baiwa kasar rancen dola biliyan 3 don farfado da tattalin arzikin kasar.

Wata tawagar IMF karkashin shugabancin Ratna Sahay, mataimakin darektan gabas ta tsakiya da sashen tsakiyar Asiya, da hukumomin Masar sun cimma yarjejeniya a tsakaninsu dangane da yarjejeniyar wucin gadi ta dola biliyan 3 don taimakawa shirin gwamnatin kasar na farfado da tattalin arzikin kasar na tsawon watanni 12 daga shekarar 2011-2012 wanda zai fara aiki daga watan Yuli,kamar yadda wata hukuma da ke Washington ta bayyana cikin wata sanarwa.

Sahay ya ce daftarin kasafin kudin na 2011-2012 ya kara bayar da damar kasahe kudade wajen samar da aikin yi da kare matalauta, yayin da za a rage irin gibin da ake kara samu. Kasafin kudin zai mayar da hankali kan ayyukan da suka shafi inganta rayuwar jama'a da zuba jari da kuma inganta ayyukan kwadago don karfafa gwiwar kara samar da ayyuka.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China