in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Asusun ba da lamuni na IMF ya bayar da rahoton hangen nesa kan tattalin arzikin kudancin Afrika
2011-05-04 10:27:52 cri

A ran 3 ga wata, asusun ba da lamuni na IMF ya bayar da rahoto cewa, ana farfado da saurin karuwar tattalin arziki a yankin Afrika dake kudu da hamadan Sahara, galibin kasashe na wannan yanki sun farfado da saurin bunkasuwar tattalin arzikinsu zuwa na shekarun farkon wannan karni.

Asusun ba da lamuni na IMF ya bayar da rahoton hangen nesa kan tattalin arzikin yankin Afrika dake kudu da hamadar Sahara na shekarar 2011 a birnin Lagos na kasar Nijeriya, inda ya yi hasashe cewa, saurin bunkasuwar tattalin arziki a wannan shekara a yankin zai kai kashi 5.5 cikin dari, kuma saurinsa na shekarar 2012 zai kai kashi 6 cikin dari. Rahoton ya kuma bayyana cewa, hauhawar farashin abinci da man fetur ta kawo kalubale sosai ga tattalin arzikin yankin, ya shawarci wasu kasashe da su tsaurara manufofin kudi.

Wakilin asusun IMF dake kasar Nijeriya ya nuna imani sosai ga makomar tattalin arzikin kasar. Amma ya kara da cewa, kalubalen da kasar Nijeriya ke fuskanta shi ne yin amfani da kudin da ta samu wajen sayar da man fetur domin kafa manyan ayyukan yau da kullum ciki har da samar da wutar lantarki da shimfida hanyoyin mota da na jiragen kasa da gina tasoshin jiragen ruwa da kuma ba da ilmi.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China