Hasashen tattalin arziki na shiyya-shiyya na IMF a kan kasashen Afrika dake kudu da hamadar Sahara ya ruwaito cewa, a yayin da akasarin tsare-tsaren bankunan shiyyar suke nuna karfinsu game da yanayin matsalar hada-hadar kudi ta duniya, tafiyar saurin bunkasuwar bashi a wasu kasashen ta kasance kuma wata matsala mai ta da hankali.
Binciken ya bayyana cewa, madaidaiciyar yawaitar bankunan kasashen Afrika a 'yan shekarun baya-bayan nan za ta kasance a wani fanni cikin sauri fiye da yadda za'a iyar daidaitawa.
Babbar darektar yankin Afrika ta IMF madam Antoinette Monsio Sayeh ta ba da sanarwar cewa, IMF ta yi hasashen cewa, bunkasuwar sarrafawa a shiyyar Afrika dake kudu da hamadar Sahara za ta ci gaba da tsayawa mai karfi a shekarar 2012.
Amma kuma, akwai bambancin hanyoyin kwarewa a cikin shiyyar, kamar sarrafawa a cikin kasashen dake samun kudin shiga madaidaici, da la'akari da tafiyar hawainiyar tattalin arziki a duniya, da kuma wasu shiyyoyin da suka samu koma-baya a kalla a cikin dan lokaci dalilin yawan fari, in ji madam Antoinette Monsio Sayeh.
Ana ganin cewa, hasashen nan gaba kan bunkasuwar kasashen Afrika dake kudu da hamadar Sahara na ta'allaka da ci gaban tattalin arzikin kasashen Kenya, Cote d'Ivoire da Zimbabwe, haka kuma zabubukan da za'a shirya a nan gaba a cikin kasashen za su tabbatar da ainihin makomar wadannan kasashe. (Maman Ada)