in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
IMF ya amince da baiwa Guinee-Conakry dalar Amurka miliyan 27.4
2013-05-22 14:31:05 cri

Kwamitin zartaswa na asusun ba da lamani na duniya IMF ya kammala aikinsa na biyu na kiyasin sakamakon tattalin arziki da kasar Guinee ta samu a cikin tsarin tallafawa samun saukin bashi na FEC, in ji wakalin asusun IMF dake kasar Guinee, Abdoul Aziz Wane a yayin wani taron manema labarai.

A cewar mista Wane, kammala wannan aiki ya taimaka ga ba da tallafi na dalar Amurka kimanin miliyan 27.4 wanda ya kai baki daya ga jimillar dalar Amurka kimanin miliyan 82.1, tun lokacin sake aiwatar da wannan tsari na saukaka samar da bashi, tsakanin hukumarsa da kasar Guinee, ganin yadda aka samu sakamako mai kyau ta fuskar cigaban tattalin arziki da matakin yaki da wasu tabi'un dake kawo rauni ga tsarin tattalin arziki da kasar ta dauka, asusun IMF ya amince da kasar Guinee, kuma a cikin watan Febrairun shekarar 2012, an samu yarjejeniyar FEC bisa tsawon shekaru uku bisa jimillar dalar Amurka miliyan 198.1 domin taimakawa shirin bunkasa tattalin arzikin gwamnatin kasar, in ji mista Wane. Haka kuma jami'in IMF ya nuna cewa, bayan shawarwarin da kwamitin zartaswa na IMF ya yi, mataimakin babban darektan IMF kuma shugaban wucin gadin na asusun ya yi wani kalami ba da jimawa ba cewa, sakamakon tattalin arzikin da kasar Guinee ta samu tare da taimakon tsarin FEC na da gamsarwa. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China