in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Asusun IMF ya yi hasashe cewa, yawan karuwar tattalin arzikin kasar Sin zai kai kashi 9.6 cikin dari a shekarar 2011
2011-01-27 17:08:47 cri

A ran 25 ga wata, asusun ba da lamuni na IMF ya bayar da rahoto game da tattalin arzikin duniya, inda ya yi hasashe cewa, yawan kasuwar tattalin arzikin kasar Sin zai kai kashi 9.6 cikin dari a shekarar 2011, kuma zai ci gaba da jagorantar bunkasuwar tattalin arzikin duniya.

Wannan ya yi daidai da abin da asusun IMF ya yi hasashe a watan Oktoba na bara kan tattalin arzikin kasar Sin. Kasar Sin ta ci gaba da daukar matsayin kasa mafi saurin bunkasuwar tattalin arziki a duniya.

A sa'i daya kuma, rahoton ya yi hasashe cewa, yawan karuwar tattalin arzikin duniya zai karu da kashi 4.5 cikin dari a shekarar 2011, wanda ya karu da kashi 0.2 cikin dari idan aka kwatanta da abin da aka yi hasashe a watan Oktoba na bara.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China