Bisa rahoton da aka gabatar, an ce, yawan kudi da kamfanin samar da man fetur da iskar gas na kasar Sin ya yi amfani da shi a fannin kirkire-kirkire ya kai dala biliyan 2.046, wanda ya zama matsayin 70 a duniya, kana ya zama kamfanin Sin daya kawai da ya shiga jerin sunayen manyan kamfanoni 100 na duniya a wannan fanni.
Rahoton ya ce, kamfanonin kasar Sin sun kara sa lura kan kirkire-kirkire yayin da ake samun ci gaba. A shekarar 2011, yawan kudin da kamfanonin kasar Sin dake cikin jerin sunayen manyan kamfanoni 1000 na duniya suka yi amfani da shi a wannan fanni ya kai dala biliyan 14.8, wanda ya karu da kashi 34.5 cikin kashi dari bisa na shekarar 2010, da kuma ya zarce da kashi 9.6 cikin kashi dari sosai bisa ga na duniya. Kana yawan kamfanonin kasar Sin da suka shiga jerin sunayen manyan kamfanoni 1000 na duniya a wannan fanni ya karu daga 15 a shekarar 2008 zuwa 47 a shekarar 2011.
Ban da wannan kuma, cibiyar Booz ta nuna cewa, bisa karuwar yawan kudi da aka yi amfani da su a fannin kirkire-kirkire a shekarar 2011, yawan kudin da kamfanonin Sin za su yi amfani da su bayan shekaru 10 zai kai dala biliyan 286.7, wanda zai kai kashi 19 cikin kashi dari bisa na duniya. (Zainab)