Ofishin yawon shakatawa na kasar Sin ya fitar da kidaddiga a ran 29 ga wata cewa, a makon hutu na sabuwar shekara ta kalandar gargajiya , kasar Sin ta karbi masu yawon shakatawa miliyan 176, ta haka, ta samu kudin Sin biliyan 101 da miliyan 400, wanda ya karu da kashi 23.6 cikin dari bisa na makamancin lokaci na bara.
Bisa kididdigar da aka yi, an ce, daga cikin daukacin kudin da aka samu a fannin yawon shakatawa, yawan kudin da kamfanonin zirga-zirgar jiragen sama suka samu ya kai kudin Sin RMB biliyan 5 da miliyan 500, kuma yawansu da hukumomin jiragen kasa suka samu ya kai kudin Sin RMB biliyan 3 da miliyan 50. Kana birane 39 na kasar Sin sun samu kudin RMB fiye da biliyan 38 daga sana'ar yawon shakatawa, kuma sauran birane da yankunan kasar sun samu kudin RMB biliyan 54.
Ban da haka kuma, wakilinmu ya samu labari daga ma'aikatar zirga-zirgar jiragen kasa ta kasar Sin a ran 29 ga wata cewa, a cikin kwanakin hutu 7 na bikin bazara, hukumomin zirga-zirgar jiragen kasa na kasar Sin sun yi jigilar fasinjoji miliyan 31 da dubu 304. Kana yawan kayayyakin da aka yi jigila ya kai ton miliyan 73 da dubu 130, wanda ya karu da kashi 2 cikin dari bisa na makamancin lokacin bara.(Lami)