in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin za ta fitar da manufofi fiye da dubu 7 a kokarin bunkasa sha'anin yawon shakatawa
2012-05-12 17:02:46 cri
A ranar Jumma'a 11 ga wannan wata, hukumar kula da harkokin yawon shakatawa ta kasar Sin ta bayyana cewa, a jajibirin "Ranar Yawon Shakatawa ta kasar Sin", hukumomi da kamfanonin da suke kula da harkokin yawon shakatawa na larduna 30 na kasar Sin za su gudanar da bukukuwa kusan dubu 1, inda za su fitar da manufofin jin dadin jama'a fiye da dubu 7 a fannin yawon shakatawa.

Ranar 19 ga watan Mayu "Rana ce ta Yawon Shakatawa a kasar Sin", wannan kuma a karo na biyu. Babban taken murnar wannan rana ta bana shi ne "jin dadin yawon shakatawa domin yin zaman rayuwa lami lafiya". Sannan ana fatan za a kaunaci yawon shakatawa da zaman rayuwa. Sabo da haka, a ranar 19 ga watan Mayu, hukumar kula da harkokin yawon shakatawa ta kasar Sin za ta shirya wani gagarumin biki a birnin Wuxi na lardin Jiangsu dake gabashin kasar domin murnar ranar yawon shakatawa ta kasar Sin ta shekarar 2012. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China