in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sha'anin yawon shakatawa na Sin zai wuce gaba a duniya a shekarar 2020
2013-02-19 14:35:56 cri
Ran 18 ga wata, mataimakin shugaban hukumar kula da harkokin yawon shakatawa ta kasar Sin Zhu Shanzhong ya bayyana a Beijing cewa, nan da shekarar 2020, sha'anin yawon shakatawa na Sin zai wuce gaba a duk fadin duniya. Musamman ta fuskar yawan fannoni daban daban da wannan harka ta shafa, da yawan yankunan da za su amfana, inganci da kuma yawan riba da za a cimma daga wajensa. Hakan a cewarsa, ya sa Sin za ta cimma burinta da ta tsara wajen bunkasa sha'anin yawon shakatawa.

A wannan rana kuma, an fidda tsarin yawon shakatawa, da hutawar jama'ar kasar na tsakanin shekarar 2013 zuwa 2020 a hukumance, wanda zai sa kaimi ga bangarorin da abin ya shafa, domin su kyautata ayyukansu na biyan bukatun dukkan jama'ar kasar Sin sama da miliyan 1300 a fannin na yawon shakatawa da kuma jin dadin hutawarsu.

Wasu masana sun nuna cewa, shimfida ayyukan da aka tsara cikin wannan shiri, da kyautata dokokin da ke kiyaye su, za su baiwa sha'anin yawon shakatawar kasar Sin damar shigewa gaba a dukkanin fadin duniya. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China