in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yawan kudin da Sin ta samu a fuskar yawon shakatawa ya kai kudin Sin Yuan biliyan 2590 a shekarar 2012
2013-01-10 10:55:50 cri
Cibiyar binciken sha'anin yawon shakatawa ta kasar Sin ta gabatar da wani rahoto a ran 9 ga wata cewa, yawan kudin da Sin ta samu a fuskar yawon shakatawa a shekarar 2012 ya kai kudin Sin Yuan biliyan 2590, wanda ya karu da kashi 15 cikin dari idan an kwatanta shi da na bara waccan.

Rahoton ya ce, ko da yake farfadowar tattalin arzikin duniya ba ta yi da tabbata ba, amma tattalin arzikin kasar Sin ya fara murmurewa a shekarar da ta gabata, harkokin yawon shakatawa na kasar Sin ya samu ci gaba da sauri kuma cikin dorewa, saboda irin kokari da dukkan ma'aikata na wannan fanni, da ma al'umma suka yi.

Kiyasin da rahoton ya gabatar na nunin cewa wannan harka za ta ci gaba da samun bunkasuwa cikin wannan shekara ta 2013, sannan gibin ciniki dangane da ba da hidima a wannan fanni shi ma zai karu.An kiyasta cewa yawan kudin da Sin za ta samu a wannan fanni zai kai kudin Sin RMB biliyan 2960 cikin shekarar 2013. (Amina)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China