Shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya, ya bayyana wannan karamci da aka yiwa 'yan wasan ne yayin wata liyafa ta musamman da aka shiryawa 'yan wasan da kuma masu horas da su a fadar shugaban kasar da ke Abuja.
An kuma karrama dukkan 'yan wasan 23 da lambar yabo ta MON, yayin da shi kuma kocin kungiyar Stevin Keshi, aka karrama shi da lambar yabo ta CON.
Bugu da kari shugaba Jonathan ya bayar da sanarwar kyautar kudi naira miliyan 10 kimanin dala 62,500 ga babban mai horas da 'yan wasan, yayin da kowa ne dan wasa ya samu kyautar naira miliyan 5 kimanin dala 31,500 da kuma fili a birnin tarayya wato Abuja.
Shugaban na Najeriya ya kuma yabawa 'yan wasan da jami'ansu bisa ga rawar da suka taka, sannan ya kalubalance su da su zage dantse don ganin sun shiga gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya da za a yi a Brazil a shekara ta 2014.(Ibrahim)