Haka nan sakamakon da aka samu, wato yadda Naijeriya ta lashe Ivory Coast da ci 2 da 1, shi ma ya ba mutane mamaki, domin idan aka kalli yadda a baya ake kwatanta kungiyoyin 2, da sakamakon da suka samu a wasannin da suka buga a baya, an ga alamar cewa Ivory Coast ita ta fi karfi. Amma sabanin yadda aka yi zato, Naijeriya ta ci wannan wasa a karshe. A yau bari mu waiwayi wannan wasa mai kayatarwa da burgewa, don tunawa da wannan nasara mai muhimmanci da kungiyar Najeriya ta samu.
Tun da farko, kungiyoyin Najeriya da Ivory Coast sun shirya sosai domin wannan wasa mai muhimmanci, ganin yadda Ivory Coast ta sanya Didier Drogba, wanda ya yi hutu a wasan da kungiyar ta buga da Aljeriya, ya dawo don jagorantar kungiyarsa. Sauran kwararrun 'yan wasan Ivory Coast da suka dawo daga hutu sun hada da mai tsaron gida Boubacar Barry, da dan wasan tsakiya na kulob din Manchester City Yaya Toure, gami da dan wasan gaba na Arsenal Gervinho.
A bangaren Najeriya kuma, mai horar da 'yan wasan kungiyar Stephen Keshi ya sanya mai tsaron gida Vincent Enyeama ya sanya alamar kyaftin, yayin da dan wasan da ya kan rike matsayin kyaftin a baya Joseph Yobo ya huta a gefen filin wasa sakamakon raunin da ya ji.
Minti 10 bayan fara wasan, an ga yadda Victor Moses na Naijeriya ya gwada kwarewar Boubacar Barry, mai tsaron gidan kungiyar Ivory Coast , da wata kwallo mai cike da basira, sai dai Barry ya hana kwallon shiga zare bayan da ya damke ta zuwa hannunsa.
Daga bisani, an ga kungiyar Naijeriya, wadda ta lashe kofin Afirka karo 2 a baya, ta yi iyakacin kokarinta don karawa da kungiyar dake kan gaba a nahiyar Afirka wato Ivory Coast. Wasan da ya samu halartar wasu taurarin kulaflikian zakarun "Premier" da dama, ya sa jama'a masu kallon wasa dubu 20 nuna farin ciki da annashuwa, tamkar suna cikin filayen wasa na Emirates ko Stamford Bridge dake Birtaniya, a maimakon Royal Bafokeng Stadium dake Rustenburg, Afirka ta Kudu, da suke ciki.
Didier Drogba ya samu damarsa ta farko bayan an wuce minti 30 ana wasan, inda ya buga wata kwallo mai tsayi daga hagu, sai dai kwallon ta karkace ba ta shiga raga ba.
Daga bisani, a minti 2 bayan da 'yan wasa suka dawo daga tsayawar wasa, Naijeriya ta ci kwallo, inda free-kick da Emmanuel Emenike ya yi ya sa kwallo ta yi shawagi har tsawon yard 25, ta kuma tsallake ganuwar da 'yan wasan Ivory Coast suka kafa tare da wuce mai tsaron gida Barry, wanda ko motsi ma bai yi ba.
Kwallon da Emenike, wanda ke buga kwallo a kulob din Spartak Moscow, ya ci ta zama ta uku a gare shi a gasa ta wannan karo, abin da ya gamsar da kungiyar sa ta Naijeriya sosai.
Yayin da mai horar da 'yan wasan kungiyar Ivory Coast Sabri Lamouchi ya gama fuska yana kallon wasa a gafen fili, kungiyarsa ta farke a minti na 50, inda Drogba ya buga free-kick daga hagu, sa'an nan Cheick Tiote na kulob din Newcastle, ya shigar da kwallo da ka daga wani wurin dake da dan nisa daga raga, wanda ta kasance kwallon farko da ya ci ga kasarsa.
Daga baya kungiyoyin 2 sun shafe tsawon lokaci suna gumurzu, inda Victor Moses ya buga kwallo daga kusurwar fili domin Brown Ideye ya shigar da ita da ka, sai dai Barry ya kama kwallon ya rungume ta. Kana a gaban ragar kugiyar Najeriya Enyeama ya sheda kwarewarsa wajen ceton kwallo a kokarinsa na hana Yaya Toure ya samu maki.
An dai ci gaba da fafatawa tsawon lokaci, inda fitattun kungiyoyin 2 suka rika kai farmaki ga junan su, da irin salon da kan zama kanun labarai da za a iya gani a jaridun kashegari.
Yayin da lokacin karshen wasa ke karotowa, Sunday Mba ya sheda hazakarsa wajen kutsa kai cikin 'yan bayan Ivory Coast, inda ya buga wata kwallon da ta keta har tsawon yardi 20, kafin tayi rawan a cikin ragar Ivory Coast, kwallon da ya tabbatar da nasarar Najeriya, ta kuma kai kasar ga wasan kusa da na karshe.(Bello Wang)