in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gwamnatin Ghana na goyon bayan dawo da martabar kulob din kasar
2013-02-08 10:58:44 cri
Shugaban kasar Ghana John Dramani Mahama ya fada a ranar Alhamis cewa, gwamnatin za ta bukaci kungiyar kwallon kafan kasar GFA da ta gudanar da bincike don gano dalilan gazawar kungiyar kwallon kafan kasar ta Black Stars na kashin da ta sha a gasar cin kofin kwallon kafan Afirka da ke gudana a kasar Afirka ta Kudu.

Da yake jawabi a wani takaitaccen biki da aka shirya game da canja matsugunin fadar gwamnatin daga Castle da ke yankin Osu zuwa sabon ofishin gwamnatin da aka gyara na Flagstaff house da ke Accra, har ila yau Mahama ya bayyana kudurin gwamnatin na bai wa kungiyar kwallon kafan kasar cikakken goyon baya wajen sake karfafa kulob din bayan gazawarsa ta lashe kofin na gasar AFCON ta shekarar 2013.

Ya ce, gwamnatin za ta yi aiki da kungiyar kwallon kafan kasar a shirin da ake na sake karfafa kulob din don tabbatar da cewa, an dawo da martabar Black Stars din cikin jerin kasashen da ke taka rawar gani a harkar kwallon kafan Afirka.

Ya kuma yaba wa 'yan wasa da jami'ansu bisa kokarin da suka yi da kuma rawar da suka taka a wasan kusa da na karshe da suka buga ranar Laraba da Burkina –Faso.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China