in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mali ta doke Ghana a wasan neman mataki na uku na gasar AFCON ta bana
2013-02-10 16:29:20 cri






Yanzu dai kasar Mali ce ta kasance ta uku a gasar cin kofin kwallon kafan nahiyar Afirka da ke gudana a kasar Afirka ta kudu, bayan da ta doke Ghana da ci 3 da 1, a wasan da suka buga jiya don neman kasar da za ta kasance a wannan matsayi.

Mali ta samu kwallon ta ta farko ne cikin mintuna 21 da fara wasan ta hannun dan wasan ta Samassa, yayin da dan wasan da ya fi kowa kwazo a wannan wasa na neman mataki na uku, wato Seidu Keita na Mali ya zura kwallo ta biyu cikin mituna na 38, kana Diarra ya kara kwallo ta uku a mintu na 90.

Ita kuma Ghana ta zura tata kwallon ne cikin mituna na 82, ta hannun dan wasanta kwadwo Asamoah, koda ya ke Wakasso ya barar wa Ghana bugun da kai sai mai tsaron gida da suka samu ana tsaka da wasan. Kuma haka aka tashi Mali na da ci 3 yayin da Ghana ke da ci 1, abin da ya baiwa Malin damar zama ta uku a gasar.

Bisa tarhin wannan gasa, dama dai Mali ta taba doke Ghana a irin wannan wasa da suka yi a gasar data gabata wadda kasashen Equatorial Guinea da Gabon suka dauki bakunci.

Yayinn da Najeriya ke shirin karawa da Burkina -Faso a yau a wasan karshe na gasar, shahararren dan kasuwannan Alhaji Aliko-Dangote, ya yiwa 'yan wasan Super Eagles alkawarin Nara milioyan 120, idan har suka lashe wannan kofin, baya ga makuden dalolin da za su samu daga bangaren hukumar kwallon kafan kasar ta Nigeria.

Sai dai kuma, sabanin bayanan da aka yi a baya cewa, shugaba Jonathan zai halarci wasan na karshe da za a buga a ranar Lahadi, yanzu an bayyana cewa, abin ba haka bane, wato dai shugaban na Najeriya ba zai halarci wasan karshen ba.

Wani labari maras dadin ji ga 'yan najeriya shi ne, 'yan wasanta biyu, wato Emmanuel Emenike da Victor Moses ba za su shiga wasan karshen ba, saboda raunin da suke fama dasu, matakin da ake ganin na iya kawo nakasu ga bangaren super Eagels din.

Sai dai mai horas da 'yan wasan Super Eagles Steven Keshi, ya ce yana da wasu 'yan wasan da za su iya maye gurbin wadannan 'yan wasa, don haka ba abin damuwa bane. Amma a yau ne zai tabbatar da cewa, ko 'yan wasan za su iya bugawa ko kuma a'a

A bangaren Burkina-Faso kuwa, yanzu dai hukumar kwallon kafan Afirka ta wanke dan wasan nan Patriopa, wanda alkalin wasan da ya jagoranci wasan da kasar ta buga da Ghana, ya ba shi kati ba bisa ka'ida ba. Saboda haka yanzu ke nan zai buga wasan da za su yi yau da Najeriya a birnin Johannesburg.

Bugu da kari kocin Burkina-Faso, ya ce ba zasu mika wuya ba ga Najeriya, duk kuwa da a cewar sa Najeriya nada zaratan 'yan wasan idan aka kwatanta su da nasa 'yan wasan, amma duk da haka za su yi kokarin ganin sun lashe wannan kofi.

Duk kasar da ta lashe kofin dai na bana, za ta samu kimanin naira miliyan 240 daga hukumar kwallon kafan Afirka, sannan za ta wakilci afirka a gasar kwallon kafan duniya da za a buga a kasar Brazil cikin shekara mai zuwa.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China