Bikin mika iko tsakanin tawagar kasa da kasa domin tallafawa kasar Mali a karkashin jagorancin nahiyar Afrika (MISMA) da hadaddiyar tawagar MDD domin shimfida zaman lafiya a kasar Mali (MINUSMA) zai gudana a ranar daya ga watan Juli da misalin karfe takwas zuwa karfe tara da rabi, bisa agogon wurin a cibiyar taron kasa da kasa dake birnin Bamako, a cewar wata sanarwar hadin gwiwa tsakanin MISMA da MINUSMA a ranar Alhamis da yamma.
A cikin bakin da za su halarci wannan biki, akwai manzon musammun na kungiyar tarayyar AU kuma shugaban tawagar MISMA, Pierre Buyoya, shugaban kwamitin kungiyar ECOWAS, Kadre Desire Ouedraogo. Haka kuma za'a samu halartar kwamishinan tarayyar AU kan zaman lafiya da tsaro, Ramtane Lamamra, manzon musammun na sakatare janar na MDD kuma shugaban tawagar MINUSMA, Bert Koenders, da kuma mataimakin sakatare janar kan ayyukan tabbatar da zaman lafiya, mista Herve Ladsous. Haka zalika, babban wakilin gwamnatin wucin gadi na kasar Mali zai halarci wannan biki. (Maman Ada)