in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Mali ya yaba da niyyar shugabannin 'yan tawayen MNLA na taimaka wa aikin rarraba takardun zabe a Kidal
2013-07-02 10:47:09 cri

Shugaban wucin gadi na kasar Mali, Dioncounda Traore ya nuna yabo kan matakin da shugabannin 'yan tawayen MNLA suka dauka na shiga aikin rarraba takardun zabe a yankin Kidal, a wani labarin da ya fito a yayin bude taro karo na biyar na gungun ba da taimako da sanya ido kan rikicin kasar Mali a ranar Litinin a cibiyar tarurukan kasa da kasa dake birnin Bamako. Shugaban kasar Mali ya jinjinawa shugabannin MNLA da suka bukaci kasancewar Kidal wani yanki na kasar Mali tare kuma da bayyana niyyarsu na taimakawa gwamnati rarraba takardun zabe a yankinsu. Mista Dioncounda ya kara da cewa, shugabannin na MNLA sun kara jaddada niyyarsu na cigaba da tattaunawa domin kawo karshen wannan rikici, da illarsa take bukatar mafita mai nagarta.

Akwai kwarin gwiwa na fatan ganin an samu zaman lafiya da jituwa tsakanin al'ummomin dake zaune a wannan yanki fiye da daruruwan shekaru.

Bisa yunkurin daidaita rikicin kasar Mali ne, aka samu cimma yarjejeniya a karon farko a ranar 18 ga watan Junin da ya gabata a birnin Ouagadougou na kasar Burkina-Faso tsakanin gwamnatin Mali da 'yan tawayen MNLA da kuma babban kwamitin hadin kan yankin Azawad (HCUA) domin gudanar da zaben shugaban kasa a ranar 28 ga watan Yuli da kuma cigaban shawarwari na tsakanin 'yan kasar Mali. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China