in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta yi kira ga bangarori daban daban na Masar da su yi kokarin magance amfani da karfin tuwo
2013-07-04 20:07:28 cri
Dangane da sanarwar da rundunar sojan kasar Masar ta bayar a kwanan baya, wato gudanar da babban zaben shugaban kasar da 'yan majalisar kasar kafin lokacin da aka tsara da kuma kafa gwamnatin rikon kwarya, Hua Chunying, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta bayyana a ranar 4 ga wata a nan Beijing cewa, kasar Sin na mai da hankali sosai kan halin da ake ciki a Masar, tana girmama zabin da jama'ar Masar suka yi.

Kasar Sin na fatan bangarori daban daban na Masar za su yi kokarin magance amfani da karfin tuwo, su kawar da sabanin da ke tsakaninsu cikin hanzari ta hanyar yin tattaunawa da shawarwari, a kokarin samun sulhuntawa da kwanciyar hankali a kasar. Jama'ar Sin da Masar sun kulla dankon zumunci a tsakaninsu. Kome halin da zai kasance, ba za a sauya huldar abokantaka da hadin gwiwa a tsakanin kasashen Sin da Masar ba.(Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China