Wata matsakaiciyar kotu ta al'umma mai lamba 2 dake nan birnin Beijing na kasar Sin, ta yankewa tsohon ministan hukumar lura da sufurin jiragen kasa Liu Zhijun hukuncin kisa tare da daurin wucin gadi na shekaru biyu kafin zartas da hukuncin, sakamakon samunsa da laifin cin hanci da rashawa, da amfani da ofishinsa domin cimma bukatu na kashin kai.
Har ila yau kotun ta haramtawa Liu, dan shekaru 60 da haihuwa shiga duk wata harka ta siyasa, ta kuma ba da umarnin kwace dukkanin dukiyar da ya mallaka. Yayin bincikenta, kotun ta gano cewa, tsakanin shekarun 1986 zuwa 2011, tsohon jami'in ya yi amfani da ofishinsa wajen samawa kansa kwangiloli, da wasu hada-hadar kasuwanci, ya kuma karbi hanci da yawansa ya kai dalar Amurka sama da miliyan 10.
Bugu da kari, kotun ta ce, wadannan laifuka da Liu ya aikata sun janyowa hukuma asara mai dinbin yawa, tare da koma baya ga hukumar da ya jagoranta a wancan lokaci, don haka ta ga dacewar yanke masa hukuncin da ya dace bisa tanajin dokokin kasar. (Saminu)