Magatakardar MDD Ban Ki-Moon ya jaddada rokonsa na kwantar da hankali, daina ta da rikici, tattaunawa da kuma kaucewa fitina a kasar Masar sakamakon shawaran da sojoji suka yi na sauke shugaba Mohammed Morsi daga kan karagar mulki da kuma dakatar da kundin tsarin mulki, yana mai kira a gare su da su gaggauta mai da mulkin hannun farar hula a kasar.
Magatakardar yana biye da abubuwan dake faruwa a kasar ta Masar sannu a hankali tare da nuna matukar damuwarsa kan sakamakon da zai biyo baya, in ji wata sanarwa da ta fito daga hannun kakakin magatakardar wanda ya ce, yana nan yana jiran ya ji alheri daga kasar.
Sai dai kuma in ji magatakardar, tsoma hannun soji a cikin al'amurran mulki abin damuwa ne, yana mai cewa, mika mulki hannun farar hula kuma yanzu a kasar ya sake shiga wani halin rashin tabbas.
Don haka, zai zama abu mai muhimmanci a mai da mulki hannun farar hula kamar yadda yake a tsarin demokradiya. (Fatimah)