A game da hanyar da Sin take bi wajen nuna goyon baya ga kasar Mali wajen samun bunkasuwa cikin lumana, Hong ya yi bayanin cewa ya zuwa yanzu, an samu kyautatuwa a fannin siyasa da tsaro a kasar Mali, sai dai ana ci gaba da fuskantar manyan kalubaloli wajen daidaita matsalolin baki daya. A matsayin aminiyar Mali, Sin na mai da hankali sosai kan yanayin da ake ciki a kasar, tare da kokarin ba da taimako ta hanyoyi daban daban, da zummar cimma burin samun bunkasuwa cikin lumana.
A kwanan baya ne dai, gwamnatin rikon kwarya ta kasar Mali ta fitar da wani shirin samun dauwamammiyar farfadowa kuma kasar Sin ta riga ta ba da agaji kan wannan shiri.Don haka take kira ga kasa da kasa da su cika alkawarinsu cikin lokaci, a kokarin kara taka rawar a zo a gani wajen sa kaimi ga sha'anin na Mali.(Fatima)