A ranar Alhamis din nan ne mai magana da yawun MDD Eduardo del Buey ya bayyana cewa, hukumar MDD dake aiki a kasar Kwadibwa ta yi tir da mummunan harin da aka kai ranar Laraba a wani kauye dake yammacin kasar ta yammacin Afirka, kana an yi kira ga ma'aikatan kiyaye zaman lafiya na MDD a yankin da su kasance cikin shiri.
Yayin jawabi da aka saba yi kowace rana ga manema labaru Edwardo del Buey ya ce, ofishin MDD a Kwadibwa ya yi tir da kisan mutane hudu a wani harin da wasu wadanda ba'a san ko su waye ba suka kai ranar Laraba, a kauyen Zilebly a yankin yammacin kasar.
Ya ci gaba da cewa, an bukaci ma'aikatan kiyaye zaman lafiya na MDD a kasar da su kasance cikin shirin ko ta kwana, su kuma kasance cikin shirin don tallafawa dakarun Kwadibwa.
Ya kara da cewa, MDD a shirye take ta taimaka wa gwamnatin Kwadibwa a yunkurinta na tabbatar da kafuwar dawowar zaman lafiya a kasar.(Lami)