in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan kasar Sin ya fara ziyarar aikinsa ta farko a ketare bayan ya hau mukaminsa
2013-05-19 16:40:22 cri
Ranar 19 ga wata da safe, Li Keqiang, firaministan kasar Sin ya tashi daga birnin Beijing, hedkwatar kasar Sin, domin fara ziyarar aiki zuwa kasashen Indiya, Pakistan, Switzerland da Jamus, wanda shi ne karo na farko da ya kai a kasashen waje bayan da ya hau kujerarsa a watan Maris a shekarar bana.

Kafin tashinsa, ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta yi bayanin cewa, ziyarar da Li Keqiang yake yi, wani muhimmin matakin diplomasiyya ne da sabuwar gwamnatin kasar Sin ta dauka kan kasashen da ke makwabtaka da ita da kasashen Turai.

A lokacin ziyararsa, firaministan zai yi shawarwari da ganawa da shugabannin wadannan kasashe 4, inda za su yi musayar ra'ayoyi dangane da al'amuran kasa da kasa da na shiyya-shiyya da ke jawo hankalinsu. Sa'an nan kuma, zai ba da lacca a kasashen 4 a lokacin wannan ziyara, inda kuma zai shaida rattaba hannu kan wasu yarjejeniyoyin yin hadin gwiwa a tsakanin Sin da kasashen 4 ta fuskar tattalin arziki da cinikayya da dai sauransu.

Kasar Indiya, zango ne na farko a kan hanyar Li Keqiang. A yayin da yake ganawa da matasan kasashen Sin da Indiya kafin ziyararsa, Li Keqiang ya ce, Sin da Indiya, muhimman makwabta ne kumma aminai ga juna. Huldar da ke tsakanin kasashen 2 na da muhimmiyar ma'ana a nahiyar Asiya da ma duk duniya, haka kuma tana da nasaba da makomar jama'arsu da yawansu ya kai biliyan 2.5. Yin zaman tare cikin lumana a tsakaninsu da girmama juna, da warware sabani yadda ya kamata za su kawo wa jama'ar kasashen 2 moriyar a-zo-a-gani, kana kuma za su samar da babban karfi wajen samun bunkasuwa da wadata a Asiya da duniya baki daya.(Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China