in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kyautata hulda a tsakanin Sin da Amurka na kawo wa duniya alheri, in ji firaministan Sin
2013-04-13 21:15:12 cri
Ranar 13 ga wata, firaministan kasar Sin Li Keqiang ya gana da sakataren harkokin wajen kasar Amurka John Kerry da ke ziyara a nan Beijing, hedkwatar kasar Sin, inda suka yi musayar ra'ayoyi dangane da zurfafa hadin gwiwar da ke tsakanin Sin da Amurka da kuma al'amuran kasa da kasa da na shiyya-shiyya da ke jawo hankalinsu duka.

A yayin ganawar, Li Keqiang ya ce, bunkasuwar dangantakar da ke tsakanin Sin da Amurka a shekaru fiye da 40 da suka wuce ta nuna cewa, moriyar bai daya ta fi sabanin da ke tsakaninsu muhimmanci, kuma nan gaba za su kara samun moriyar bai daya a fannoni da dama. Don haka kasar Sin na son ta hada hannu da Amurka, su girmama juna, kara samun amincewar juna, tinkarar sabanin da ke tsakaninsu, da kuma habaka hadin gwiwar da ke tsakaninsu, a kokarin kafa kyakkyawar hulda ta sabon salo tsakanin manyan kasashe.

Shi ma a nasa bangaren, Kerry ya ce, kasar Amurka na son yin kokari tare da Sin wajen kara kyautata tsarin hadin gwiwa, habaka hadin gwiwa don samun moriyar juna, da tinkarar kalubalolin da duk duniya ke fuskanta da kuma al'amuran da ke jawo hankali tare. (Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China