A yayin ganawar, Li Keqiang ya ce, yanzu kasashen Sin da Zambiya na fuskantar sabuwar dama wajen bunkasa kansu. Don haka kasar Sin na son yin kokari tare da Zambiya wajen kara samun amincewar juna, a kokarin samun kyakkyawan tabbaci ta fuskar siyasa. Sa'an nan kuma, in ji shi, ya kamata kasashen 2 su hada manufofinsu na tattalin arziki da na bunkasa kasa tare, su habaka mu'amala a tsakaninsu ta fuskar tattalin arziki da cinikayya, su zurfafa hadin gwiwarsu ta fuskar tattara da kuma zuba jari, da ma kokarin tabbatar da ganin muhimman ayyuka sun ba da jagora kuma sun zama abin misali. Haka kuma, firaministan ya ce, kasar Sin za ta kara bai wa Zambiya taimakon fasaha da horas da kwararrunta, a kokarin kyautata kwarewar Zambiya ta samun bunkasuwa da kanta ta hanyoyi daban daban, tare da kyautata zaman rayuwar jama'ar kasar. Har wa yau Li Keqiang ya yi fatan cewa, Zambiya za ta ci gaba da kiyaye halaltattun hakkokin masana'antun kasar Sin da ke kasar.
Haka zalika, firaministan kasar Sin ya nuna cewa, inganta hadin gwiwar abokantaka a tsakanin Sin da Afirka, wani muhimmin tushe ne ga kasar Sin a harkokin waje. Kasar Sin tana son hada kai da kasashen Afirka, su dauki hakikanin matakai wajen bude sabon shafi na yin hadin gwiwa a tsakaninsu.
A nasa bangaren kuma, shugaban Zambiya Michael Sata ya gode wa kasar Sin bisa taimako da goyon bayan da take ba kasarsa a shekarun baya. A cewarsa Zambiya za ta ci gaba da tsayawa kan manufar kasar Sin daya tak a duniya, don haka tana son kara yin hadin gwiwa da kasar Sin a fannonin tattalin arziki da cinikayya, aikin gona, zirga-zirgar jiragen sama, yawon shakatawa da dai sauransu.(Tasallah)