Har wa yau kuma, a yayin ganawar, Li Keqiang ya ki yarda kan ba da kariyar cinikayya ta hanyoyi daban daban, kana ya jaddada muhimmancin habaka fannonin yin hadin gwiwa a tsakanin Sin da Faransa. A cewarsa kuma, kasar Sin za ta ci gaba da mara wa kasashen Turai baya wajen tinkarar matsalar bashi da ke addabarsu.
A nasa bangaren kuma, François Hollande ya ce, ya kamata kasashen 2 su himmantu wajen tafiyar da harkokin duniya yadda ya kamata da tinkarar kalubale iri daban daban. Kasar Faransa tana son zurfafa da habaka hadin gwiwar da ke tsakaninta da Sin a fannoni daban daban, da kin yarda da ba da kariya kan harkokin cinikayya tare, a kokarin samun moriyar juna da nasara tare. (Tasallah)