Shugaban kungiyar AU na wannan karo, kuma firaministan kasar Habasha Hailemariam Dessalegn ya ba da jawabi cewa, ko da yake an riga an samu ci gaba kan aikin kawar da matsananciyar yunwa, akwai bukatar a kara yin kokari wajen fuskantar karancin abinci da kuma matsananciyar yunwa.
Ya kuma yi kira ga gamayyar kasa da kasa da su yi hadin gwiwa wajen ba da taimako ga Afirka kan fuskantar kalubalolin karancin abinci da matsananciyar yunwa da sauyin yanayi ya kawo wa Afirka, da kuma ba da tabbaci ga kasashen Afirka wajen kawar da mawuyacin halin kafin shekara ta 2025.
Bugu da kari, shugabar kwamitin kungiyar tarayyar kasashen Afirka Dlamini Zuma ta bayyana cewa, ban da dukufa kan samar da karin hatsi, ya kamata kasashen Afirka su kara zuba jari wajen inganta fasahohin ajiyewa da kuma gyara hatsi, don rage barnatar da abinci. (Maryam)