Kakakin majalisar gudanarwa ta kasar Amurka ya bayyana ra'ayinsa kan harin ta'addanci da aka kai a gundumar Shanshan ta jihar Xinjiang ta kasar Sin, inda ya bukaci kasar Sin da ta daidaita batun bisa doka, kuma ya ce, kasar Amurka na sa ido sosai kan labarin da aka bayar kan cewa, wai ana nuna bambanci ga 'yan kabilar Uygur da jama'a musulmai da kuma daukar matakan kayyade zamansu.
Game da batun, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Madam Hua Chunying ta bayyana a yau jumma'a 28 ga wata, cewar kasar Sin bata ji dadi kan yadda kasar Amurka ta yi shachi fadi kafin ta gano ainihin lamarin, kana da yadda ta zargi manufofin kabilu da addinai na kasar Sin.
Don haka Sin na bukatar kasar Amurka da ta magance daukar ma'auni iri biyu a kan batun yaki da ta'addanci .(Kande Gao)