in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kamfanin jiragen sama na "Senegal Airlines" aka ba nauyin jigilar maniyatan kasar Senegal in ji firaministan kasar
2011-08-05 15:15:01 cri
Firaministan kasar Senegal, Souleymane Ndene Ndiaye ya bada wata sanarwa a ranar Alhamis cewa kamfanin jiragen sama na kasar wato "Senegal Airlines" zai yi jigilar maniyata a wannan shekara zuwa Makka.

Kamfanin da ya soma gudanar da harkokinsa a cikin watan Janairun shekarar 2010 ne zai dauki nauyin jigilar maniyatan kasar Senegal a karon farko.

A shekarar bara, Kamfanin jiragen sama na kasar Spaniya "Air Europa" ya yi jigilar maniyatan kasar Senegal kimanin 8200.

A sakamakon wani babban taron da aka kebe kan batun Hajin wannan shekara, firaministan kasar ya bayana cewa kamfanin "Senegal Airlines" ne zai kasance wanda zai yi jigilar musulman kasar Senegal kuma kudin tikitin jirgi ya dan karu zuwa Sefa miliyon 1,235 maimakon miliyon 1,100 a shekarar data gabata.

Tashin farko na maniyatan zuwa kasa mai tsarki zai fara daga ranar 14 zuwa 25 ga watan Oktoba kuma zasu dawo daga ranar 10 zuwa 27 ga watan Nuwamba.(Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China