Ministan tsaron kasar Yamousa Camara a jiya Alhamis ya sanar cewa, sojojin kasar a shirye suke su dau mataki idan har shawarwarin da ake yi a yanzu haka da kungiyar 'yan tawayen Azawad ya ci tura.
Yace, sake karbe garin kidal ba wani abin damuwa ba ne. Idan dai har Faransa ta yi amannar cewa, za su iya wannan aiki ba tare da an zubar da jini ba, wanda hakan yana da kyau. Sai dai kuma Sojojin kasar a shirye suke na yin yaki domin kwato Kidal.
Ministan tsaron ya fadi hakan ne a lokacin ziyararsa a cibiyar horo ta kungiyar tarayyar Turai dake garin Koulikoro.
Wannan ziyarar ita ce ta farko da Ministan tsaron kasar Mali ya kai a cibiyar da kungiyar Tarayyar Turai ta kafa domin amfanin sojojin Mali.(Fatimah Jibril)