Bayan shigar da dutsen Tianshan a ciki, yanzu kenan, a kasar Sin na da wuraren tarihi 44 da aka shigar da su cikin jerin sunayen wuraren tarihi na duniya.
An yi wannan taron kasa da kasa karo na 37 na wuraren tarihi da aka gada daga kaka da kakanni daga ranar 16 zuwa ranar 27 ga wata a birnin Phnom Penh da na Siem Reap da ke kasar Cambodiya, kuma za a duba takardun roko da kasashe mambobi suka mika don neman shigar da wuraren tarihi 31cikin jerin sunayen wuraren tarihi na duniya. A ranar 22 ga wata, za a duba bukata da kasar Sin ta gabatar, don shigar da gonaki kan tuddai na kabilar Hani ta lardin Yunan na kasar Sin cikin jerin sunayen wuraren tarihi na duniya.(Bako)