in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Najeriya zai tattauna tare da takwarorinsa na kasashen Afirka kan batun fashin teku a mashigin tekun Guinea
2013-06-23 20:47:54 cri
Shugaban tarayyar Najeriya Goodluck Ebele Jonathan zai tashi zuwa birnin Yaounde na kasar Kamaru, domin halartar taron koli na shugabannin kasashen yammaci da tsakiyar nahiyar Afirka, kan tsaron gabar tekun Guinea, wanda za'a yi a ranar litinin 24 ga wata. An dai shirya wannan taro ne a daidai lokacin da matsalar fashin teku a wannan yanki ke kara zama ruwan dare.

Bisa sanarwar da mai baiwa shugaban kasar shawara na musamman kan harkokin watsa labarai Reuben Abati ya fitar, shugaba Jonathan zai tattauna tare da ragowar shugabannin kasashe mambobin kungiyar ECOWAS, da na kasashen tsakiyar Afirka, dangane da wani sabon shiri na daukar matakan shawo kan matsalar 'yan fashin teku, da kiyaye zaman lafiya a wannan yanki na gabashin gabar tekun Guinea.

Cikin tawagar shugaba Jonathan daga Nijeriya akwai ministan shari'a Mohammed Adoke, da ministan kula da harkokin cikin gida Abba Moro, da ministan ma'aikatar sufuri Alhaji Idris Umar, da kuma karamin minista a ma'aikatar tsaro Erelu Olusola Obada. Ragowar masu dafawa shugaban kasar baya sun hada da babban kwamandan rundunar sojin ruwa Vice Admiral Joseph Ezeoba, da kuma Mista Patrick Akpobolokemi, darekta janar na hukumar sa ido da kiyaye zaman lafiyar yankin tekun Najeriya.

Har wa yau kuma, shugaba Goodluck Jonathan zai yi shawarwari tare da takwaransa na kasar Kamaru Paul Biya, game da batutuwan da suka jibanci kasashen Najeriya da Kamaru, ciki har da tsaron kan iyaka, da kuma zamantakewar 'yan Najeriya a kasar Kamaru.

Ana kuma sa ran shugaba Jonathan zai gana da 'yan Najeriya mazauna kasar ta Kamaru kafin komawarsa babban birnin tarayya Nijeriya Abuja, a ranar Talata 25 ga wata.(Murtala)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China