Da misalin karfe 8 da rabi na safe na ranar 24 ga wata, agogon Beijing, Mr. Xi Jinping, babban sakataren kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, shugaban kasar, kuma shugaban kwamitin tsakiya na soja na kasar ya ziyarci cibiyar sarrafa zirga-zirgar kumbon 'yan sama jannati dake Beijing, inda ya yi hira da 'yan sama jannati uku, wato Nie Haiheng, Zhang Xiaoguang da madam Wang Yaping na kasar Sin wadanda yanzu suke aiki a kumbo kirar Tiangong mai lamba 1 a sararin sama.
Yayin hirar, Xi Jinping ya nuna gaisuwa ga wadannan 'yan sama jannati a madadin kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, majalisar gudanarwa ta gwamnatin kasar, kwamitin tsakiya na soja da al'ummar kasar Sin baki daya.
A ran 11 ga wata ne, kasar Sin ta harba kumbon 'yan sama jannati kirar Shenzhou mai lamba 10 cikin nasara. Sannan a ran 23 ga wata, 'yan sama jannati suka hada shi da kumbo kirar Tiangong mai lamba 1 da hannu, wadannan 'yan sama jannati uku sun shiga kumbo kirar Tiangong mai lamba 1 inda suka fara yin aikin gwaji a ciki. (Sanusi Chen)