Shugaba Xi wanda shi ne babban sakatare na kwamitin tsakiya na jam'iyyar, ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a wani shirin karawa juna sani da ofishin harkar siyasa na kwamitin tsakiya na jam'iyyar ta gabatar ranar Talata da yamma, in ji wata sanarwa da aka bayar yau Laraba 26 ga wata.
Ya ce, tarihi muhimmiyar hanya ce ta koyon darasi wadda ta zama wajibi, musamman ma ga manyan jami'ai domin su samu koyon tarihin jami'yyar CPC wacce ta yi shekaru 92 da kafuwa da kuma Jamhuriyar Jama'ar Kasar Sin (PRC) wacce ke da shekaru 64 da kafuwa, a kokari da ake yi na kara kawowa kasar bunkasa bisa turbar tsarin gurguzu.
Shugaba Xi na mai cewa, shirin karawa juna sani da aka yi ranar Talata, mai taken 'fasali da salon gurguzu, mai tsarin kasar Sin' za ta kara fargar da jami'ai ne dangane da sauye-sauye a kasar Sin, gami da bunkasuwa da kuma dorewa.
Xi ya jaddada cewa, wajibi jam'iyyar ta zamo tana wakilci a fuskar muhimman bukatu na mafi yawan jama'ar kasar Sin, wanda kuma ta dalilin hakan ne jam'iyyar ke samun goyon bayan jama'a tun shekaru tale-tale.
Ya kuma yi kira da a kara himma da nufin kara gina jam'iyyar domin a samu karfafa amincin jama'a a salon gurguzu bisa tsarin kasar Sin. (Lami Ali)