Bisa labarin da wakiliyar gidan rediyo kasar Sin ta aiko mana, an ce, za a gayyaci manyan jami'an kiwon lafiya na kasashen Afirka 51 da jakadunsu da ke nan kasar Sin, jami'an kungiyoyin kasa da kasa, ciki har da kungiyar kiwon lafiya ta kasa da kasa da bankin duniya da su halarci taron, ta yadda za su iya amfana da fasahohin da kasar Sin ta samu wajen tallafawa kasashen Afirka a fannin kiwon lafiya, kuma za su tattauna kan yadda za a kara yin hadin gwiwa kan harkokin kiwon lafiya tsakanin Sin da kasashen Afirka a cikin sabon yanayin da ake ciki yanzu.
Shekarar da muke ciki shekara ce ta cika shekaru 50 da kasar Sin ta tura rukunonin likitoci zuwa kasashen Afirka. Sabo da haka, a yayin wannan taron, za a kara tattaunawa kan yadda za a yi hadin gwiwa wajen tsara manufofin kiwon lafiya kan harkokin horar da kwararru, yada fasahohin kiwon lafiya da magance karuwar masu kamuwa da cututtukan yau da kullum a kasashen Afirka. Kana kuma, za a tattauna kan yadda kasashen Sin da Afirka za su yi koyi da kuma amfani da fasahohin zamani na kiwon lafiya daga kasashe masu wadata domin ciyar da harkokin kiwon lafiya a kasashen Afirka gaba. (Sanusi Chen)