Tsohon shugaban kasar Afrika ta Kudu Nelson Mandela ya koma gidansa bayan ya kwashe dare guda a wani asibitin kasar domin yi masa binciken lafiya, in ji fadar shugaban kasar Afrika ta Kudu.
'Likitocin dake gudanar da wannan binciken lafiya, sun bayyana cewa, babu wani dalilin ta da hankali a halin yanzu.' in ji kakakin fadar shugaban kasar Mac Maharaj a kwanan nan, a lokacin da aka kwantar da tsohon shugaban kasar a asibiti. Wannan shi ne karo na biyu a kwantar da Mandela a asibiti a cikin watanni uku.
Nelson Mandela mai shekaru 94, an kwantar da shi asibiti a ranar 8 ga watan Disamban shekarar 2012 dalilin fama da ciwo a huhu. A ranar 15 ga watan Disamban bara, an yi masa tiyata cikin nasara kan wata matsala a madaciya.
An bai wa Nelson Mandela damar komawa gidansa a ranar 26 ga watan Disamba tare da samun jinya a gidansa bayan zaman asibiti na kwanaki 19 wadanda ya kasance zamansa a asibiti mafi tsawon tun bayan shekarar 2001.
Mandela ya shugabanci kasar Afirka ta Kude ne daga shekarar 1994 zuwa shekarar 1999, kuma ya kwashe shekaru 27 na zaman yari domin yaki da bambancin launin fata a kasar Afrika ta Kudu. Bayan fito daga kurkuku a shekarar 1990, bayan shekaru hudu ya zama shugaban farko na bakar fata a kasar Afrika ta Kudu, haka kuma ya samu kyautar Nobel ta zaman lafiya a shekarar 1993. (Maman Ada)