Majalisar dattijan kasar Masar za ta cigaba da aikinta har zuwa ganin an shirya zabubukan 'yan majalisar dokoki, domin dokar kasa ba ta tabuwa, in ji fadar shugaban kasar Masar a cikin wata sanarwa ta ranar Lahadi da yamma a matsayin maida martani ga matakin da babbar kotun kasa ta dauka na soke kwamitin Choura dake matsayin majalisar dattijai.
Babbar kotun ta bayyana harancin aikin Choura a ranar Lahadi, da aka baiwa ikon duba dokoki, dalilin rashin majalisar dokoki, tare da kwamitin da ya rubuta kundin tsarin mulki, bisa zargin cewa, an taka kundin tsarin mulki, dokar da ta ba da dama ga zaben majalisar dattijai, har da matakan da suka kai ga zaben mambobin kwamitin da ya rubuta dokar kasa da ta janyo takadama da aka amince da ita bayan zaben raba gardama na watan Disamba.
Kotun shari'a ta amince da majalisar dattijai da ta tsaya wajen cigaba da aiki kafin zaben wata sabuwar majalisa. Bisa amsar da ta ba da kan wannan mataki, fadar shugaban kasa ta bayyana cewa, sabon kundin tsarin mulki ya samu amincewa a cikin watan Disamban da ya gabata ta hanyar zaben raba gardama, wannan wajibi ne hukumomin kasa su kare da girmama wannan dokar kasa.
Fadar shugaban kasa da kotun shari'a na cikin ja in ja tun lokacin da aka rushe zauren 'yan majalisa dalilin rashin girmama kundin tsarin mulki na wannan doka da ta shafi zaben wannan zaure, kwanaki kadan bayan zaben Mohamed Morsi a matsayin shugaban kasar Masar a cikin watan Yunin shekarar 2012. (Maman Ada)