in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sin ya gana da babban sakataren MDD
2013-06-19 18:50:06 cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da babban sakataren MDD Ban Ki-moon a ranar 19 ga wata a nan birnin Beijing, inda ya bayyana cewa, kamata ya yi MDD ta bi manufar samun zaman lafiya da bunkasuwa, da bada ra'ayoyi da gudanar da ayyuka cikin adalci.

Xi Jinping ya nuna cewa, ana samun sauye-sauye a fadin duniya a yanzu, muddin ana bukatar a warware matsaloli da kalubalen da aka fuskanta a duniya, tilas ne a bi hanyar hadin gwiwa da samun moriyar juna. Game da wannan fanni, ya kamata MDD ta taka muhimmiyar rawa.

Kana Xi Jinping ya jaddada cewa, kasar Sin za ta ci gaba da sa kaimi ga warware matsalolin kasa da kasa cikin lumana, da nuna goyon baya ga MDD wajen cimma burin bunkasuwa da aka tsara a shekarar 2000. Kuma tana son yin kokari tare da bangarori daban daban wajen tinkarar batun sauye-sauyen yanayi da sauran batutuwan duniya, ta haka ne za a bada taimako wajen samun zaman lafiya a duniya da bunkasuwar dan Adam.

A jawabinsa Ban Ki-moon ya taya jama'ar kasar Sin murnar cimma burinsu na farfado da al'ummar kasar Sin. Kana ya bayyana cewa, cimma burin kasar Sin zai kawo babban tasiri ga MDD har ma da fadin duniya.

Ban da wannan kuma, Ban Ki-moon ya ce, MDD ta bukaci kasar Sin da ta kara taka muhimmiyar rawa wajen tinkarar halin sauye-sauye da duniya ke fuskanta da kuma matsalolin kasa da kasa da na yankuna. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China