Bisa labarin da aka samu, an ce, lamarin ya faru ne a yankin mahakar ma'adinai ta Bambari, mai nisan kilomita 440 daga Banji, babban birnin kasar. Ya zuwa yanzu, an riga an tabbatar da mutuwar mutane 37, dukkansu 'yan asalin kasar, yayin da mutane da dama suka samu raunuka, kuma ake tsoron samun karin wadanda ka iya rasuwa cikin majiyyatan.
Kasar jamhuriyar Afirka ta Tsakiya dai na da wadatar ma'adinai, amma yanzu, ana gudanar da ayyukan hakar lu'u-lu'u da zinari ne ba tare da amfani da na'urori na zamani ba. Bugu da kari, cikin jimillar al'ummar kasar miliyan 4.4, yawan wadanda suke wannan aiki na hakar ma'adanai bai wuce kaso 15 bisa dari ba. (Maryam)




