Kakakin Magatakardar MDD Martin Nesirky wanda ya fitar da wannan sako cikin wata sanarwa,ya ce ofishin na shawartar gwamnatocin kasashen game da tilasta ma wadannan 'yan gudun hijira da suka tsere zuwa kasashen su komawa gida domin halin da ake ciki yanzu ya tsananta.
Ofishin ya yi tunin cewa a lura da ka'idojin ba da agajin jin kai da kuma mafaka a game da al'amarin dake faruwa a kasar Afrikan ta tsakiya kafin a yi tunanin ko ya dace a mayar da'yan gudun hijiran,domin a cewar Mr Nesirky fadace fadacen watannin nan da suka gabata yayi sanadiyar raba mutane akalla 173,000 da gidajen su sannan kuma kusan mutane 50,000 suka yi gudun hijira zuwa kasashen Jamhuriyar demokradiya ta Kongo,Chadi da Kamaru.
Mr Nesirky ya kuma bayyana cewa tuni dai a ranar litinin din daya gabata kwamitin tsaro na MDD ya fitar da sanarwar nuna matukar damuwar ta game da wannan tashin tashina dake wanzuwa a kasar Afrikan ta tsakiya.
Sanarwar in ji shi ya bayyana kiran da kwamitin mai wakilai 15 suka yi na bukatar a aiwatar da yarjejeniyar N'Djamena wanda ya amince da kudurin kungiyar tarayyar tattalin kasashen Afrika ta tsakiya a ranar 18 ga watan da ya shige wato Afrilu.(Fatimah Jibril)