Baya ga haka, taron zai maida hankali kan matsalar tsaro dake adabar yankin Sahel, musammun ma game da yaki da ta'addanci da aikata laifuffukan kasa da kasa, kamar yadda tarurukan hadin gwiwa da mu'amala na UFL da kwamitin hadin gwiwa na hafsoshin sojojin na CEMOC suka yi.
A cikin jawabinsa a taron kwamitin hafsoshin rundunar sojojin kasashen mambobin CEMOC, da ya gudana ranakun 10 da 11 ga watan Yuli a birnin Nouachoutt na kasar Mauritaniya, babban janar na sojojin kasar Aljeriya, Ahmed Gaid Salah yayi Allah wadai da al'amuran tashin hankali da rikicin kasar Mali ya janyo bisa matsalar tsaro a wannan shiyya, tare da jaddada cewa ya zama wajibi a daidaita wadannan matsaloli cikin gajeren lokaci ta yadda 'yan kasar Mali za su maido da zaman lafiya da tsarin dimokuradiya. (Maman Ada)