Sakamakon shiga tsakanin da gwamnatin kasar Amurka ta yi ya sa Benjamin Netanyahu da Mahmoud Abbas sun maido da shawarwarin zaman lafiya ido da ido a birnin Washington a farkon watan Satumba na shekarar 2010, amma an dakatar da shawarwarin bayan makonni da dama saboda Isra'ila ta ki yarda da tsawaita wa'adin hana gina matsugunan Yahudawa a yammacin gabar kogin Jordan. Kullum Palesdinu ta mayar da daina gina matsugunan Yahudawa a yammacin gabar kogin Jordan da gabashin Kudus a matsayin daya daga cikin sharuddan da ta gindaya wajen maido da shawarwarin zaman lafiya a tsakaninta da Isra'ila.
Benjamin Netanyahu ya kara da cewa, a shekaru 4 da suka wuce, ya yi ta tsayawa tsayin daka kan yin shawarwari a tsakanin kasarsa da Palesdinu ba tare da wani sharadi ba. A ganinsa, gindaya sharadi kafin a yi shawarwari ya kan lalata zaman lafiya cikin sauri. A shekaru 4 da suka wuce, gindaya sharadi ya sa ba a cimma wata madafa ba a yayin shawarwarin zaman lafiyar.
Har wa yau kuma, Benjamin Netanyahu yana ganin cewa, muhimmin dalilin da ya haddasa rikici a tsakanin Isra'ila da Palesdinu shi ne Palesdinu ta dade tana kin amincewa da kasancewar kasar Yahudawa. (Tasallah)