Bisa wannan shirin da aka tsayar, Isra'ila za ta gina gidaje 1600 a yankin Ramat Shlomo dake arewa maso gabashin birnin Jerusalem. Ban da wannan kuma, ma'aikatar ta yi shirin amincewa da sauran shirye-shirye guda 2 wajen gina gidajen da yawansu ya kai 2700 a Jerusalem.
Palasdinu ta yi Allah wadai da matakin da Isra'ila ta dauka. Babban jami'in yin tattaunawa na Palasdinu Saeb Erekat ya lura da cewa, wannan matakin da Isra'ila ta dauka ya sabawa dokar kasa da kasa kuma zai kawo illa ga aikin shimfida zaman lafiya tsakanin bangarorin biyu. Kuma ya yi kira ga kasar Amurka da ta mayar da martani kan wannan batun tare da goyon bayan Palasdinu wajen kafa kasar kanta.
A wannan rana kuma, jami'i musamman mai daidaita aikin shimfida zaman lafiya a yankin gabas ta tsakiya Robert Serry ya yi kira ga Isra'ila da ta dakatar da wannan shiri, yana cewa, wannan shirin zai kawo illa ga kokarin da kasashen duniya suka yi wajen farfado da shawarwarin sulhuntawa tsakanin bangarorin biyu.(Amina)