in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta nuna sassaucin ra'ayi ga batun Iran ta halarci taron kasa da kasa game da batun Syria
2013-05-21 20:41:32 cri
Kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin Hong Lei ya bayyana a ranar 21 ga wata a nan birnin Beijing cewa, kasar Sin ta amince da duk wani irin kokarin warware batun Syria ta hanyar siyasa, kana ta nuna maraba da kiran da kasashen da abin ya shafa suka yi da a gudanar da taron kasa da kasa kan batun Syria. Kuma kasar Sin ta nuna sassaucin ra'ayi ga Iran da Saudiyya da su halarci taron.

Ban da wannan kuma, Hong Lei ya bayyana cewa, a halin yanzu, bangarorin da abin ya shafa suna kiyaye yin mu'amala kan harkokin taron. A ganin kasar Sin, ana bukatar kasashen dake yankin, musamman kasashen da za su yi tasiri game da halin kasar Syria ke ciki da su nuna goyon baya ga kokarin da ake yi na warware batun Syria. Kasar Sin tana son yin kokari tare da kasa da kasa wajen warware batun Syria cikin adalci, da kuma lumana. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China