Sin ta yi kira ga Isra'illa da Syria da su kwantar da hankali
Game da harin da Isra'illa ta kai wa kasar Syria a kwanakin baya, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying ta bayyana a ranar 6 ga wata a nan birnin Beijing cewa, kasar Sin ta yi kira ga bangarorin da abin ya shafa da su yi la'akari da tabbatar da zaman lafiya a yankin, kwantar da hankali, da kuma magance daukar matakan da za su tsanantar da halin da ake ciki. Kasar Sin ta ki amincewa da yin amfani da karfin soja, a ganin Sin, ya kamata a girmama ikon mallakar kasa. (Zainab)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku